Najeriya: Sabbin Ministoci sun sha rantsuwar kama aiki | BATUTUWA | DW | 21.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Sabbin Ministoci sun sha rantsuwar kama aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da membobin majalisar ministocinsa tare da nada sabon mukamin karamin ministan albarkatun mai a majalisar mai ministoci 43.

A wani abun da ke zaman alamun tashi zuwa mataki na gaba, a wannan Laraba ne Shugaba Muhammad Buhari ya rantsar da majalisar ministoci tare da kara sabbin ma'aikatu guda biyar. Daya bayan daya dai ministocin dama shi kansa sakatare na gwamnatin Najeriyar, suka dauki rantsuwar kamun aiki bisa mukaman da ke da tasiri ga makomar kasar.


Babban buriin gwamnati acewar fadar shugaban kasar, dorawa kan aikin tabbatar da tsaro tare kuma da iya kai wa ga samar da aiyyukan yi ga matasa kusan Milliyan biyun da ke suka gama makaranta ba tare da samun aikin yi ba. Kuma daga dukkan alamu ko bayan dorawa bisa jiga-jigan manufofi na gwamnatin guda uku, shugaban kasar ya kuma kara sabbin ma'aikatun da ke da burin kula da ci gaban kasar.

Nigerias Präsident Buhari und sein Vize beim APC-Parteitag (Novo Isioro)

Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo sun yi alkawarin inganta rayuwar al'uma


Sabbin ministocin dai sun hada da Ike Chukwu Oga da aka nada a matsayin karamin ministan Ma'adinai na kasar da Mohammed Musa Bello, ministan babban birnin tarraya na Abuja. An tura Godswill Akpabio ya zuwa ma'aikatar Niger  Delta a yayin kuma da Festus Keyamo zai zamo karamin minista a wurin. Adamu adamu zai ci gaba da mukaminsa na ministan ilimi a yayin da Emeka Nwajiba ya zamo karamin minista a wurin .  An kuma nada Sabo Nanono ministan Noma a yayin kuma da Mustapha Shehuri zai zama karamin minista a wurin. Maryam Katagum ce aka bai wa karamar minista a  ma'aikatar Ciniki ta kasar a yayin kuma da Richard Adebayo zai jagoranci ma'aikatar.

 

Chris Ngige dai ya ci gaba a ma'aikata ta Kwadago a yayin kuma da Tayo Alasoadura zai taimaka masa. Zainab Shamsu na Ma'aikatar Kudi da tsare-tsare na tattalin arzikin da kafin yanzun ke zaman ma'aikatu biyu a matsayi na minista a yayin kuma da  janar Bashir Magashi ya zamo minista na tsaro. LaiMohammed ya ci gaba a matsayin Ministan yada Labarai haka kuma Rotimi Ameachi ya dora a ma'aikatar Sufuri ta kasar. Babatunde Fashola ya zauna a Ma'aikatar gida da aiyyuka a yayin kuma da aka balle harka ta wutar lantarki aka bai wa Injiniya Saleh Mamman a matsayi na minista. Abubakar Malami dai shi ne ministan Shari'a, haka Suleman Adamu ya ci gaba a ma'aikatar Ruwa a yayin kuma da aka kara darajar Hadi Sirika zuwa babban minista a Ma'aikatar Sufuri na sama.

 

Sadiya Faruk dai ce ministar sabuwar ma'aikatar Jinkai da agajin gaggawa ta kasar a yayin kuma da Rauf Aregbesola ya zamo ministan cikin gida. Maigari Dingyadi ya zamo sabon minista a sabuwar ma'aikatar 'yan sanda a yayin kuma da Shugaba Buhari ya ci gaba da zama ministan Mai na kasar. Babban aikin da ke gaban majalisar dai na zaman kawo sauyi da 'yan kasar ke da bukata ga muhimman batutuwan tsaro da harkokin noma da inganta tattali na arziki dama bin doka.


 

Sauti da bidiyo akan labarin