Najeriya: PENGASSAN da NUPENG sun janye yajin aiki | Labarai | DW | 09.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: PENGASSAN da NUPENG sun janye yajin aiki

A cewar Babatunde Oke mai magana da yawun kungiyar PENGASSAN an tsaida ayyukan da suke yi a fadin kasar ta Najeriya, saboda adawarsu da shirin sauya fasalin ma'aikatar.

Nigeria National Petroleum Corporation Öl-Industrie Korruption

Kamfanin NNPC a Abuja Najeriya

Ma'aikata a kamfanin albarkatun man fetir a Najeriya sun tsaida ayyukan da suke yi a ranar Laraba saboda nuna adawarsu da shirin sauyi fasalin ma'aikatar, da rarrabata zuwa rassa bakwai, abin da ke nuna cewa za a iya samun ci gaban matsalar da ake fiskanta ta wadannan albarkatu a wannan kasa da ke zama ja gaba wajen fitar da albakatun a tsakanin kasashen Afirka.

Wannan na zuwa ne bayan da ita ma kungiyar kananan ma'aikata ta NUPENG ta fito da yin adawa da shirin ministan kasa a ma'aikatar albarkatun man na Najeriya Ibe Kachuku na karkasa kamfanin dan samun riba, abin da kungiyar ta ce ministan na daukar matakai ne a kamfanin ba tare da tuntubarsu ba. Sai dai a ranar Alhamis din nan kungiyoyin biyu sun bayyana janye yajin aikin da suka fara.