1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Oby Ezekwesili ba za ta tsaya takara ba

Muhammad Bello AH
January 24, 2019

A Najeriya a baya-bayan nan, mace me kamar maza Oby Ezekwesili da ta tsaya takarar shugaban kasa, kuma ta tsaya kai da fata kan neman a zabe ta ta bayyana cewar ta janye daga takarar.

https://p.dw.com/p/3C7yk
Initiative Bringbackourgirls Nigeria
Hoto: DW/K. Gänsler

Janyewar da madam Oby Ezekwesili ta yi daga takarar da ta nuna jajircewar za ta yi don neman kujerar shugabancin Najeriya, bai bai wa wasu mamaki ba, ko da yake wasu sun bayyana mamakinsu. Tsohuwar ministar dai da ke da nufin bai wa mata karfin gwiwar shiga a dama da su a siyasar kasar, ta ce ta janye ne domin ta hangi cewar hada karfi da wasu jam'iyyun ne mafita wajen fafatawa da manyan jam'iyyun kasar na APC da PDP.  A maganar da ake yi dai yanzu, alkaluma na nuna cewar bayan ayyana janyewar takarar da madam Oby Ezekwesili din ta yi, sai nan da nan Jam'iyyarta The Allied Congress Party of Nigeria, ta yi shelar aniyar hada karfi da Jam'iyya mai mulki ta APC don goyon bayan takarar Muhammadu Buhari.