1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na kwaso 'yan kasarta daga Libiya

November 30, 2017

A wani abun da ke zaman kama hanyar cika umarni gwamnatin Tarayyar Najeriya na kwashe daukaci na 'yan kasar da ake zargin cinikinsu a kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/2oZOH
Libyen Migranten Flüchtlinge Boot
Hoto: picture-alliance/dpa/E.Morenatti

Masu ruwa da tsaki da aikin kwasar dai na can sun dukufa da nufin tabbatar da kai karshen cigaba da kwashe daukaci na 'yan kasar da ke a Libiya.Kama daga jeri na zanga-zanga zuwa muhawara a dandalai dabam-dabam dai, daga dukkan alamu zuciya ta yi baki a cikin Tarayyar Najeriya sakamakon kallon ciniki na 'yan kasar a Libiya.

To sai dai kuma tuni gwamnatin kasar ta kama hanyar warware lamura tare da umarnin shugaban kasar na kwashe daukaci na al'ummar Tarayyar Najeriyar da ke can a kasar Libiyan.

Ya zuwa ranar Alhamis din dai gwamnatin kasar ta ware jirgin da ke sahu a kalla daya da nufin aikin jigilar da ake saran za ta kammala tare da kwashe kusan 'yan kasar 11,000 da ke fuskantar matsala a kasar a fadar Khadijah Bukar Abba da ke zaman karamar ministan harkokin waje ta Najeriya da kuma ke jagorantar aikin jigilar.

Mittelmeer Migranten und Flüchtlinge in Schlauchboot
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Diab

Mafi yawan da suka iso filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke birnin Legas da kuma ke zaman cibiya ta karbar bakin dai na cikin halin taggayara da nuna alamun gajiya a fadar Sadiya Umar Faruk da ke zaman babbar kwamishinar kula da 'yan gudun hijirar Tarrayar Najeriyar.

Tuni  dai mahukuntan na Abuja suka kaddamar da shirin sake inganta rayuwar bakin Libiyan a cikin wani shiri da ke samun hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin da kuma jihohinsu na asali.

Kai karshen matsalar Libiyan dai na iya kaiwa ga sassauta kwararar ta matasa ya zuwa Turai ci rani da ma mutuwar daruruwansu a teku. Matsalar da ko bayan kasashen na Afirka da ke Kudu da Hamada ta Sahara ta kuma adabbi su kansu Turawan Yamman.