Najeriya na hukunta masu karya dokar corona | Labarai | DW | 13.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya na hukunta masu karya dokar corona

A Najeriya, mahukunta a birnin Abuja, sun kaddamar da kotun tafi-da-gidanka da za ta yanke hukunci nan take a kan duk wani da aka kama da laifin karya dokokin corona.

Matakin ya zo ne sakamakon yadda wannan cuta ke bazuwa a Najeriyar, inda a hukumance ake da alkaluman sama da mutum dubu da 700 da coronar ta kashe, wasu sama da dubu 143 ma na fama da ita.

Najeriyar wacce ta fi ko wace kasa a nahiyar Afirka yawan jama'a, na fama da karancin cibiyoyi da ma kayan gwajin wannan cuta, abin ma da ya sanya tababa a kan adadin da hukumomin ke sanarwa dangane da wadanda cutar ta shafa.

Akwai dai dokar sanya takunkumin kare baki da hanci da kuma nesa-nesa da juna, kamar sauran sassa na duniya, sai dai galibi mutane bijire wa dokar a fadin kasar.

Duk wanda aka kama ba tare da takunkumin na corona ba, ko ma ya sanya shi ba bisa ka'ida ba, zai biya tarar Naira dubu biyu nan take.

Cikin watan jiya ne kuwa Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wata dokar daurin watanni shida ga duk wanda ya taka doka daya daga cikin dokokin coronar.