Najeriya na duba wata mara lafiya daga Afirka ta Kudu saboda Ebola | Labarai | DW | 11.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya na duba wata mara lafiya daga Afirka ta Kudu saboda Ebola

Fargabar shigar wa Najeriya cutar Ebola ya sanya ma'aikatan lafiya aikin kula da baƙi masu shiga ƙasar ba dare ba rana.

Mahukunta a fannin lafiya a Najeriya sun bayyana cewar a ranar Alhamis ɗin nan za su gudanar da gwajin ƙwayar cutar Ebola kan wata 'yar asalin ƙasar Afirka ta Kudu da hanya ta biyo da ita ta ƙasar ta Najeriya saboda a cewar mahukuntan akwai alamun da ke nuna cewar tana iya harbuwa da ƙwayoyin cutar bayan aikin da ta yi a ƙasashen Guinea da Saliyo.

Matar 'yar asalin Afirka ta Kudu wacce ba a bayyana sunanta ba, ta shigo birnin Legas ne na Najeriyar daga Moroko ana kuma dubata bisa zargin ko tana ɗauke da ƙwayoyin wannan cuta a cibiyar da aka tanada dan masu cutar ta Ebola.

Matafiyar a lokacin da take cike takardar da aka tanada dan yin bincike da saukarta a Legas ta bayyana cewar tana fama da amai da gudawa dukkansu kuma alamu ne da ke nuna cewar tana iya harbuwa da ƙwayoyin na cutar Ebola.