1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da miyagun kwayoyi saboda tsaro

August 4, 2020

A cigaba da kokarin tunkarar matsalar rashin tsaron da ke tashi da lafawa a sassan Tarayyar Najeriya dabam-dabam, majalisar tsaron kasar ta ce za ta karkatar da hankalinta zuwa yaki da shan muggan kwayoyi.

https://p.dw.com/p/3gPuh
Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Taron majalisar tsaron Najeriya, ya yanke shawarar yaki da shan miyagun kwayoyiHoto: Reuters/Nigeria Presidency

Sannu a hankali dai Tarayyar Najeriyar yi kaura daga kasar da ke karba ta miyagun kwayoyi, ya zuwa sabuwar matattara ta sarrafa kwayar a yankin Yammacin Afirka. Kuma ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta ce batun shan kwayoyin, na da ruwa da tsaki da ta'azzarar rashin tsaron walau a yankin Arewa maso Gabas da ke fama da 'yan ta'adda ko kuma dan uwansa na Arewa maso Yamma da ke fuskantar rikicin 'yan ina da shan jini.
A wani zaman da ta gudanar a Abuja, majalisar ta ce ta gano kamfanonin sarrafa muggan kwayoyi har 17 a sassa dabam-dabam, cikin kasar da ke taka rawa ga ta'azzarar matsalar tsaro. Babagana Mungono dai na zaman mashawarcin tsaro na gwamnatin kasar da kuma yac e miyagun kwayoyin na tasiri a batun matsalar tsaron Najeriyar a wurare da dama.

Nigeria Razzia Drogenlabor
Samamen yaki da shan kayan mayeHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Kama daga dillallai ya zuwa ma'aikatan tsaro da ke taimaka musu, sannan da uwa uba 'yan kwayar dai, Tarayyar Najeriyar ta ce tana kallo na sababbi na dabarun tunkarar matsalar da ke ta yaduwa a ko'ina, a kokari na samar da zaman lafiya cikin kasar a halin yanzu. Duk da cewar dai an samu lafawar rikici a jihohi irin na Zamfara da Katsina, kudancin jihar Kaduna ya sake daukar zafi ya zuwa yanzu a cikin rikicin da Mungunon ya ce na siyasa ne.

Afrika Nigeria Borno Professor Babagana Umara Zulum
Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara ZulumHoto: Government House, Maiduguri, Borno State

Da yammacin wannan Talatar ne dai, aka tsara wata ganawa a tsakanin kungiyar gwamnonin kasar da mashawarcin na tsaro da nufin nazarin ikirarin gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum da ya zargi sojojin kasar da wani harin da ya nemi halaka shi a Baga, kafin wata ganawar da ake shirin yi a tsakanin gwamnan da shugaban kasar a nan gaba.

To sai dai kuma a fada ta Mongunon ba shi da hurumin yanke hukunci har sai an kamalla ganawa a tsakanin shugaban kasar da gwamnan  Bornon. Harin na gwamnan Bornon dai daga dukkan alamu na shirin sauyin rikicin na tsaro, inda gwamnonin jihohi na kasar 36 suka yanke hukuncin ganawa da shugaaban kasar da manyan hafsoshi na tsaron da nufin neman mafita, a cikin zargin da ke tayar da hankali da nuna jan aikin da ke gaban 'yan mulki na kasar game da batun rashin tsaron.