1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude zauren majalisar dokokin Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
October 9, 2018

Majalisar dokokin Najeriya ta koma bakin aikinta bayan kwashe fiye da watanni biyu tana rufe, inda ake zaman tankiya kan yunkurin tsige shugbanin majalisar da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa.

https://p.dw.com/p/36EwV
National Assembly in Abuja, Nigeria
Hoto: DW

'Yan majaisun dokokin Najeriyar dai sun yi tururuwa zuwa zauren majalisar a cike da annuri da ma sa ran abin da ka iya faruwa, amma ana fara zama sai suka shiga zaman sirri na 'yan mintina a majlisar dattawa, bayan fitowarsu sun ci gaba da zama tare da karanta kudurori har 15 da shugaban Najeriya ya ki sa hannu a kansu, inda a karshe suka amince da kafa kwamiti da zai duba batun.

Koda yake mutuwar guda daga cikin 'yan majalisar wakilai wato Honourable Funke Adedoyin ta sanya daukar mataki bisa al'ada na hana taso da duk wani batu da ke da sarkakiya, abin da ya hana dago batun tsige shugabannin majalisar kamar yadda aka yi tsammani. sai dai da alamu tana kasa tana dabo a kan batun tsige shugabanin majalisar da kowanne bangare ya ja daga a kai.