Najeriya: Kwanaki 500 da sace ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 27.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Kwanaki 500 da sace 'yan matan Chibok

Albarkacin wannan rana Kungiyar BBOG mai fafitikar ganin an ceto 'yan matan ta gudanar da taruka dama Jerin gwano a Abuja Domin kawo goya bayansu ga 'yan matan.

A Najeriya a kwana a tashi a wannan Alhamis kwanaki 500 da Kungiyar Boko Haram mai fada da makamai a kasar ta sace 'yan matan makarantar skandire ta garin Chibok su sama da 200 a cikin Jihar Borno. A ranar 14 ga watan Aprilun shekarar bara ne dai kungiyar ta kame 'yan matan su 276 a dai dai lokacin da suke shirin gudanar da jarabawar kammala karatun sakandire.

Tun a wancan lokaci dai 52 daga cikin wadannan 'yan mata sun yi nasarar kubuce wa daga hannun Kungiyar ta Boko Haram wacce ke ci gaba da rukon sauran 219 wadanda har kawo yanzu ba'a da duriyarsu. Kuma duk kokarin da sojojin kasar ke yi na neman ceto wadannan 'yan mata a dazukan da ake zaton kungiyar na tsare da su har kawo yanzu ya ci tura.

Albarkacin wannan rana ta cikwan kwanaki 500 da sace 'yan matan garin na Chibok, kungiyar BBOG mai fafutkar ganin an ceto wadannan yara na gudanar da taruka daban-daban dama jerin gwano a birnin Abuja domin kawo goyan bayansu ga wadannan 'yan mata dama tunatar da duniya halin da su ke ciki.