1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kurakurai a shari'ar Boko Haram

September 17, 2018

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Human Rights Watch ta zargi Najeriya da tafka kurakurai a cikin shari'ar daruruwan mutanen da take tsare da su a bisa zargin kasancewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/352B6
Nigeria Boko Haram
Hoto: DW/Al-Amin Suleiman Mohammad

Ya zuwa yanzu dai kusan 'ya'yan kungiyar dubu biyu ne ke fuskantar shari’a a cibiyoyi dabam-dabam na Tarrayar Najeriyar bayan kama su. To sai dai kuma wata shari’ar da gwamantin kasar ta fara a shekarar da ta shude a barikin Wawa da ke cikin jihar Niger dai, daga dukkan alamu na shirin baya da kura sakamakon rashin cika jeri na ka’idoji a tunanin kungiyar ta Human Rights Watch mai kare hakkin dan Adam. Wani rahoton da ta fitar da safiyar wannan Litinin 17 ga watan Satumba ya ce shari’ar ta saba ka’idoji da daman gaske sannan kuma ta karya 'yanci da mutunci na wadanda ake tuhumar  a fadar Aniete Ewang da ke zaman jami’ar Kungiyar a Tarrayar Najeriyar da kuma ta ce ta bi diddigi bisa jerin shari’un. A gaba daya babu dabaru na tuhumar manyan masu laifi daban da masu kanana. Gaba daya an yi gaggawa wajen yin shari’un, kuma mafi yawansu masu kananan laifi ne wadanda ake jin sun ba da taimakon da babu tada hankali a cikinsa.

Nigeria Arbeiter einer Ölfirma durch Boko Haram entführt
Wasu daga cikin mutanen da ake tsare da su a Najeriya a bisa zargin kasancewa 'yan Boko Haram.Hoto: Reuters/Sahara Reporters


Duk da cewar akwai wadanda ake tuhuma da  manyan laifuka irin na sata ta mutane  da kisan kai, amma dai ba a ba da fifiko kan wannan ba, ta yadda mutane da ke neman adalci za su tabbatar da an samu haka. Haka kuma ba a bai wa al’ummar damar kallo ko taka rawa ko ma shaida a yayin shari’ar ba. Ba a ba da dama ga masu tunanin neman hukunci  sun gamsu da abin da ya faru ba. Shari’ar ta barikin Wawan da ta gudana a cikin watan Yulin da ya shude dai na zaman matakin farko na maida martani na gwamnatin tarrayar a bisa kari na matsin lambar neman mutunta hakkin na 'ya'ya na kungiyar ta Boko Haram. Ana kuma kallon sabo na binciken na Human Rights Watch na iya sanyaya gwiwar Abujar da ke neman kari na agaji na kasashe wajen a cikin sabon imanin na sauya salo a cikin takaddamar mai tasiri.

Tschad Armee Soldaten Zeremonie
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Batun na take hakki dai na zaman karfen kafa a tsakanin Tarayyar Najeriyar da cika burinta na samu na makaman yaki a bangaren tsohuwar gwamnatin kasar. To sai dai kuma a fadar Barrister Buhari Yusuf, da kamar wuya iya cika ka’idojin shari’u irin na ta’addanci ko dai a cikin Tarayyar Najeriya ko ga duk wata kasa ta duniya da ke tsakiyar wannan yaki. Duk da cewar dai sama da 'ya'yan kungiyar 1669 ne dai ke tsare a barkin Wawa, da kyar da gumin goshi aka kai ga kamalla shari’ar 800. Daruruwan 'ya'yan kungiyar dai na fatan adalci a cikin jerin shari’un a kokari na neman sulhu da kai karshen rikicin da ya dauki shekara da shekaru.