Najeriya: Kotu ta daure sojan da ya yi kisa | Labarai | DW | 02.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Kotu ta daure sojan da ya yi kisa

Wata kotin sojan Najeriya ta yanke hukuncin kaso na shekaru bakwai kan wani soja da ya kashe Umar Alkali wani farar hula a kasuwar "Monday Market" ta Maiduguri

A Najeriya wata kotun sojojin kasar ta yanke wa wani sojin kasar hukuncin zaman wakafi na tsawon shekaru bakwai bayan da ta same shi da aikata laifin kisan wani mutun mai suna Umar Alkali ba da gangan ba a ranar 23 ga watan Disambar shekara ta 2015 a kasuwar "Monday Market" da ke a tsakiyar birnin Maiduguri.

Rundunar sojin Najeriya ce ta sanar da wannan labari a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Larabar jiya, inda ta ce sojojin wanda ba ta bayyana sunansa ba, ya musanta aikata wannan laifi a gaban kotu, yana mai da'awar cewa ya buda wuta ne kan mutuman a matsayin matakin kare kansa da sauran abonana aikinsa sojoji, bayan da mutuman ya yi yinkurin kwace bindigar wani daga cikin sojojin. 

Sai dai kotun ta yi watsi da wannan hujja tasa a bisa hujjar cewa ya yi amfani da karfin da ya wuce kima. Ana dai kallon matakin kotun a matsayin wani babban ci gaba a wannan kasa inda ba safai ake hukunta sojojin da ke cin zarafin fararan hula ba.