Najeriya: Kokarin tattabar da tsaro a Niger Delta | Siyasa | DW | 24.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Kokarin tattabar da tsaro a Niger Delta

Manyan hafsoshin sojan Najeriya sun hallara a yankin Niger Delta na Najeriya domin magance kai hare-hare kan bututun tura iskar gas da na danye mai.

Wannan yunkuri da hafsoshin sojan na Najeriya ke yi dai na da nasaba da irin yadda sha'anin tsaro a yankin na Niger Delta ke kara tabarbarewa tun bayan da a makonnin da suka gabatar 'yan bindigar yankin suka koma kai hare-hare kan bututan da ke tura mai da iskar gas zuwa sassan kasar daban-daban. Tawagar hafsoshin dai ta hada da hafsan hafsoshin kasar Janar Abayomi Gabriel Olonisakin da shugaban sojan kasa Janar Tukur Buratai da takwaransa na sojin ruwa Vice Admiral Ibok Ibas da na rundunar sojin sama Air Marshal Sadiq Abubakar.

Symbolbild Soldaten Nigeria

Sojoji sun gargadi 'yan bidinga kan fasa butun mai da iskar gas

Tuni dai hafsan hafsoshin sojan na Najeriya Janar Olonisakin ya ce sun aike da kwakkwaran sako ga 'yan bincigar na Niger Delta inda ya ce ''wannan hare-hare ba abu ne da kasa za ta aminta da su ba saboda barna ce ake yi wa kadarori da kasa ke dogaro da su a harkokin tattalin arziki, kuma akwai hanyoyi da dama da 'yan bindigar za su bi don bayyana bukatunsu ga gwamnati.''

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers wadda ke zaman guda daga cikin jihohin na yankin Niger Delta cewa ya yi wannan ta'annati da 'yan bindigar ke aikatawa zagon kasa ne ga tattalin arzikin Najeriya. Maimakon farwa kadarorin gwmanati da na kamfanonin hakar mai, Gwamna Wike ya cewa ya yi duk mai wani korafi to kamata ya yi ya mika kukansa ga hukumar da abin ya shafa don shre masa hawaye maimakon daukar doka a hannunsa.

Nigeria Soldaten in Damboa

Gwamnatin Najeriya na son a dakatar da kai hare-hare kan wajen tono danye mai

A daura da wannan taron da manyan jami'an rundunonin sojin kasar, gwamnonin sun ce za su yi wani zama na musamman da gwamnatin tarayyar kasar domin shata hanyoyin da za su bi wajen kawo karshen wannan matsala. Najeriya dai na dogaro da dumbin arzikin mai da ke yankin na Niger Delta domin samun kudaden da ta ke tafiyar da lamuranta na yau da kullum.

Sauti da bidiyo akan labarin