1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamen 'yar TikTok a Kano Najeriya

Nasir Salisu Zango LMJ
January 31, 2023

Rundunar 'yansanda a jihar Kano, ta bayar da belin shahararriyar tauraruwar nan ta TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya. An dai kama Murja ne a jajiberin ranar da ta shirya bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

https://p.dw.com/p/4MuyJ
Najeriya | Kano | TikTok
Jaruman TikTok na fuskantar matsala a jihar Kano da ke NajeriyaHoto: DW Eigendreh

An dai kama Murja Ibrahim Kunya ne a Asabar din da ta gabata a wani Otel da ke Kano, inda take saukar bakinta da ta gayyato domin taya ta bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta. Dama dai an jima ana kuka da ita, kan irin kalaman batsa da ashariya da take yawan saki a shafukanta na tiktok. Sai dai wasu na ganin cewar idan an bi ta barawo, to ya kamata abi ta mabi sahu. Yanzu haka dai lauyan da ya jagoranci yin karar Murja ya bayyana cewar nan gaba kadan za a kai ta asibiti domin tabbatar da cewar a cikin hayyacin ta take sakin wadannan faya-fayan bidiyo, wadanda ko kadan yake cewar ba su dace da mai hankali ba.  Barr Badamasi Suleman Gandu shi ne ya jagoranci zauren malamai na jihar Kano, domin yin karar wasu taurari da mawaka da suke ganin suna wuce makadi da rawa wajen gabatar da harkokinsu wanda ka iya lalata tarbiya.

Facebook, Twitter, Instagram, TikTok
Kafafen sada zumunta na zamani, na janyo cece-kuce. Sai dai suna da nasu amfaninHoto: Hideki Yoshihara/AFLO/IMAGO

A jawabinsa kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kanon SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya nunar da cewa, korafe-korafe da ake samu a kan Murja sune makasudin kamata. Ana ta bangaren Murja Kunya ta ce ta yi nadama, kuma za ta kiyaye harshenta a nan gaba. Sai dai wasu na ganin cewar wannan mataki da aka dauka a kan Murja tamkar nuna wariya ne, kasancewar akwai wadanda aka zarge su da laifin tare amma ita kadai aka kama. Aliyu Dahiru Aliyu dan jarida ne mai kuma fashin baki kan al'amuran yau da kullum, ya ce tabbatar da adalci shi ne suma sauran a kamo su. Fitowar TikTok da sauran wasu shafukan sada zumunta dai ta samar da saukakkar hanyar isar da sako ga miliyoyin mutane ba tare da kaidi ba, lamarin da kan sa ana samun matsalolin na sakin abubuwan da kan jawo cece-kuce.