1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gobara ta tashi a ofishin INEC

Ahmed Salisu
April 18, 2020

Gobara ta tashi a hedikwatar hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wato INEC da ke Abuja, fadar gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/3b5dA
Nigeria Terror Anschlag Abuja
Hoto: Reuters

Kakakin hukumar zaben Aliyu Bello ya ce inda gobarar ta shafi sashin da ke sanya idanu kan jam'iyyun siyasu na kasar wanda inda a nan ne bangaren yada labarai na hukumar yake.

Wakilinmu DW a Abuja Uwais Abubakar Idris wanda ya ziyarci wajen da gobarar ta kama ya ce takardu da ke cikin ginin sun kone sai dai a zantawarsa da kakakin hukumar ya shaida masa cewar takardun ba masu muhimmanci bane, kuma ya ce nan gaba kadan za a fara bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

Tashin gobara a ofishin na INEC din a aka samu a yau dai na zuwa ne bayan da aka samu abu makamancin haka a ofishin Akanta Janar na kasar da kuma ofishin yi wa kamfanoni rijista wato CAC.