Najeriya: Gobara ta kashe 'yan gudun hijira
March 27, 2018Talla
Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso gabashin Najeriya na cewa akalla mutane biyar sun mutu yayin da wata gobara ta barke a wani sansani makare da 'yan gudun hijira dubu 55.
Gobarar ta tashi ne sakamakon wutar da aka rura don dafa abinci a sansanin. Wutar ta dau akalla sa'oi uku ta na ci, ta kuma haddasa kone tantuna da sauran kayyaki da dama.
A yanzu dai tuni hukumomin ba da gaji da ke kula da yankin suka garzaya da wadan da suka jikkata daga gobarar. Garin na Rann da ke kan iyaka da Kamaru na da akalla mutane dubu 80 kuma jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun sha fuskantar hare-haren mayakan Boko Haram.