Najeriya: Jama'a sun gudu bayan ficewar sojin Chadi
January 4, 2020Daruruwan 'yan Najeriya mazauna garuruwan Gajiganna da Monguno da sauran garuruwan kusa da iyaka da kasar Chadi sun tsere daga garuruwan nasu a ranar Juma'a zuwa Maiduguri, bayan da sojojin kasar Chadi da ke yaki da Boko Haram a yankin suka fice daga cikinsa a ranar Juma'ar. Watanni tara da suka gabata kenan da kasar ta Chadi ta girke sojoji dubu 12 a garuruwan Najeriya na kan iyaka da ita, da zimmar yaki da Boko Haram.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an gano sojojin kasar ta Chadi a cikin tankokin yaki da sauran motoci sun ratsa gadar da ta raba biranen Kousseri na Kamaru a kan hanyarsu ta komawa gida Ndjamena.
Kakakin rundunar sojin kasar ta Chadi Kanal Azem Bermandao ya ce a yanzu babu sojin Chadi daya a Najeriya, sun fice bayan da wa'adin aikinsu ya cika, inda yanzu za su koma sansanoninsu da ke a yankin tafkin Chadi. Wani dan kato da gora a birnin na Mungono da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce suma sojojin Najeriya da ke aiki da na Chadi a yankin sun fice daga cikinsa.