1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya nada shugaban ma'aikatan fadarsa

May 13, 2020

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya tabbatar da nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin babban shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3cAQU
Nigeria Abuja | Neuernannter Stabschef Ibrahim Gambari
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

Tsohon mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kana tsohon ministan harkokin waje na Najeriyar, Farfesa Ibrahim Gambari ya maye gurbin marigayi Abba Kyari da ya rasu a karshen watan Afrilun da ya gabata. Mai shekaru 75 dai, ana saka ran Gambari zai nuna kwarrwarsa a kokarin ceto kasar da ke halin matsalar tattalin arziki da tabarbarewar tsaro. Batun matsalar tattalin arzikin dai, ya kara yin kamari a kasar sakamakon annobar cutar coronavirus.

Biyayya da hidima

Dayake jawabi ga manema Labarai, Farfesa Gambari ya bayyana cewa ya shirya tsaf da nufin hidima ga shugaban kasar yana mai cewa: "Ina godiya ga Allah mai girma da kuma shugaban kasar da ya bani damar yi wa shugaban kasata hidima. Yanzu nake shirin kamun aiki. Zan yi biyayya, kuma babban burina shi ne yi wa shugaban kasar hidima iya karfina.

Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

A karon farko tun bayan tsaida harkoki na gwamnati, an gudanar da taron majalisar zartarwar kasar wanda aka yi shi daga nesa domin bayar da tazara sakamakon annobar cutar coronavirus.

Taron majalisar zartaswar ta Najeriya, ya amince da rage ma'aunin kasafin kudi a cikin tsarin da yake kallon raguwar tattalin arziki da sama da kaso hudu cikin 100, kamar yadda ministar kudin kasar Zainab Shamsuna ta tabbatar. Wannan ne dai karo na farko da kasar ke neman sake farfadowa daga illar COVID-19 da ta tsayar  da al'amura na gwamnati na tsawon kusan watanni biyu. Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da Najeriyar ta shiga mataki na biyu na rayuwa cikin COVID-19, a cikin halin matsi da rashin tabbas ga makomar al'ummar da suka share shekaru suna dogaro da hajjar man fetur.

Mayar da hankali kan noma

Taron ya kuma amince da zaftare yawan man fetur din da kasar ke fatan hakowa daga ganga miliyan biyu da dubu 180, ya zuwa miliyan daya da dubu 900 kullum. Haka kuma Najeriyar ta rage kiyasi na farashin man daga dalar Amirka 57 kan kowace ganga zuwa dalar Amirkan 25, yayin kuma da kasar ke saka ran cin bashi na kusan Tiriliyan biyar da nufin rage radadin annobar.

Najeriyar dai ta ce tana shirin daukar jeri na matakai da suka hada da sake mai da hankali zuwa harkar noma, harkar da take fatan za ta maye gurbin man fetur da farashinsa ya koma baya. Alhaji Sabo na Nono dai, na zaman ministan noma na kasar da kuma ya ce an amince da wani sabon bashin dalar Amirka miliyan dubu daya da miliyan 200 da za a yi amfani da su a cibiyoyin fara bunkasa harkar noma na zamani, a wasu kananan hukumomi sama da 600 na kasar.