Najeriya: faduwar Naira na barazana ga tattalin arziki | Siyasa | DW | 14.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: faduwar Naira na barazana ga tattalin arziki

Faduwar darajar takardar kudi ta Naira na barazana ga cigaban tattalin arzikin kasar musamman ma a wannan lokacin da tattalin arziki na duniya ke fuskantar kalubale.

Tattalin arziki a Nigeria ya fada wani irin yanayi na tsaka mai wuya inda farashin kayayyaki ke cigaba da tashin gwauron zabi. Hukumar kididdiga ta kasar ta ce an sami hauhawar farashin kayayyakin masarufi a cikin kasar da misalin kaso 15 cikin 100. Wannan hali da ake ciki ya sanya 'yan kasuwa a kasar irinsu Alhaji Kasumu Kurfi da ke hada-hadar kudade da sanya hannun jari a Nigeria cewar rabon da a fuskanci irin wannan matsalar yau shekaru 6 kenan.

Nigerdelta Angriff Rebellen

Tada kayar bayan 'yan bindiga a wuraren da ake tono mai kalubale ne babba ga tattalin arzikin Najeriya

Bisa ga bincike da DW ta gudanar, kamfanoni na cikin gida da na waje sun tafka asarar da ta kai kimanin Naira miliyan dubu 200 cikin watannin shidda da suka gabata sabili da rashin mu'amalar dalar Amurka da sauran kudaden waje kuma 'yan kasuwa a kasar na ba cewar hakan zai iya zartawa.

Äthiopien Gipfel Afrikanische Union - Muhammadu Buhari

'Yan Najeriya na son shugaban kasar Muhammadu Buhari ya fidda hanyoyi da za su sassauta halin kuncin da suke ciki

Masu fashin baki na kasuwanci a Najeriya na ganin karancin kudaden kasashen waje a hannun 'yan kasuwa da masu zuba jari musamman ma a farashin gwamnati na daya daga cikin abubuwan da suka sanya 'yan kasuwa kauracewa kasar wanda hakan babban nakasu ne ga tattalin arzikin kasar. Wani abu har wa yau da ke barazana ga tattalin arzikin kasar baya ga lalacewar darajar Naira shi ne karyewar farashin mai da kuma lalata bututun man da tsagerun Niger Delta ke yi a wuraren da ake hako mai. Wannan yanayi da ake ciki dai yanzu haka ya sanya talakawan Najeriya kokawa kan irin mawuyacin halin da suke ciki inda suke shawartar gwamnatin kasar da ta yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin ta bijiro da hanyoyin da za a yi amfani da su wajen sassauta irin tsananin da ake fuskanta a halin yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin