Najeriya: el-Zakzaky zai je Indiya neman magani | Labarai | DW | 05.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: el-Zakzaky zai je Indiya neman magani

Wata babban kotu da ke jihar Kaduna ce ta bai wa jagoran kungiyar 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky izinin fita daga kasar domin ya sami damar ganin likita

Lauyoyin malamin ne suka nemi a bai wa malamin izinin fita bayan da ya shafe shekaru a tsare cikin yanayi na rashin lafiya. A shekarar 2015 aka kama malamin tare da mai dakinsa a yayin wani artabu a tsakanin mabiyansa da rundunar sojin Najeriya a garin Zariya da ke jihar Kaduna a arewacin kasar.

Tun daga wancan lokacin mabiya malamin ke gudanar da gangami don janyo hankalin gwamnati na sakin malamin ba tare da anyi nasara ba. A lokuta da dama da ake gudanar da ire-iren wadannan gangamin,  an yi ta samun barkewar rikici da ke janyo asarar rayuka.