Najeriya: EFCC ta zargi alkalin kotu ma′aikata | Labarai | DW | 03.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: EFCC ta zargi alkalin kotu ma'aikata

A Tarayyar Najeriya hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci ta zargi alkalin kotun kula da da'ar ma'aikata da laifin cin hanci wanda tuni ta gabatar da bayanan a gaban wata kotu domin hukunci.

Nigeria Plakate und Aufkleber gegen Korruption (DW/K. Gänsler)

Yaki da cin hanci a Najeriya

Hakan ya fito ne a cikin wasu bayanai da hukumar da ke kula da cin hanci ta Najeriya EFCC ta mika wa wata kotu a Najeriya kan zargin da ake yi wa mai shari'a Umar da laifukan cin hanci, inda ya nemi da a biya shi miliyan 10 na Naira kwatankwacin sama da Euro dubu 23 daga wani da ake zargi wanda shari'arsa ke a hannun wannan alkalin.

Bayanan da hukumar ta EFCC ta gabatar sun kuma nunar cewa, ko a shekara ta 2012 ma alkalin da ake zargi ya karbi Naira miliyan daya da dubu 800 ta hanyar daya daga cikin abokan aikinsa, kuma duk kudaden sun fito ne daga mutumen guda da takardun shari'arsa ta zargin cin hanci ke a hannun wannan alkali.

Shi dai wannan alkalin na Najeriya mai suna Umar an damka mishi jagorancin wannan kotun da ke kula da da'ar ma'aikata, da kuma sauran bayannai na jabu da manyan ma'aikatan gwamnati ke yi dangane da dukiyoyinsu wanda kundin tsarin mulki ya tilasta musu yi, kuma shi ne ya wanke shugaban majalisar dattawa ta Najeriya Bukola Saraki a bara bayan da aka zargeshi da laifin cin hanci lokacin yana gwamnan jihar Kwara daga shekara 2003 zuwa 2011.

Wannan shari'a ta Bukola Saraki wanda ke a matsayi na uku na shugabanci a Tarayyar Najeriya na a zaman babban kalubale na yaki da cin hancin da Najeriyar ta sa wa gaba.