Najeriya: EFCC ta kama makusancin Atiku | Siyasa | DW | 05.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Kama kusa a yakin zaben jam'iyyar adawa ta PDP

Najeriya: EFCC ta kama makusancin Atiku

Ana cece-kuce a Najeriya biyo bayan kame mataimakin daraktan cibiyar yakin neman zabe na jamiyyar adawa ta PDP inda jam'iyyar ta ce kamun Turaki Kabiru wata barazana ce ga dimukradiyya tana mai cewa dole a sake shi.

A Najeriya babbar jamiyyar adawa PDP ta fusata game da kama wani jigo a jamiyyar wato mataimakin darakta yakin neman zabe dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar Atiku Abubakar.

Hukumar EFCC na zargin Tani Kabiru Turaki da zuba kudaden da suka zarta kima wajen yakin neman zabe da suka kai Euro milynan 150 a kasar. Sai dai tuni jam'iyyar PDP ta yi fatali da kamun tana mai bayyana cewar ba zata razana ba, inda ta bayyana kamun da cewar na a matsayin wata babbar barazana ce ta siyasa ganin cewar sun lashi takobin kalubalantar sakamakon zaben da ya ayyana Buhari a matsayin shugaban kasa a gaban kuliya.

A baya dai hukumar EFCC ta bayyana cewa ba makawa  zata duba irin kudadden yakin neman zabe da ‘yan siyasa ke kashewa domin bisa doka akwai mizanin da aka suka cancanta 'yan siyasar su kai ga kashewa. Sai dai kamun na zuwa ne kwanaki a gabanin zaben gomnoni da 'yan majalisun jihohi da ake shirin gudanarwa wanda kuma bisa al'ada kudi kke taka muhimmiyar rawa a cikin yakin neman zaben. 

Sauti da bidiyo akan labarin