1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Rikicin dakatar da 'yan majalisa a Zamfara

December 22, 2025

'Yan majalisar dokokin Jihar Zamfara da ke Najeriya guda tara sun ce kusan shekaru biyu ke nan tunda gwamnan jihar ya sa aka dakatar da su har yanzu ba a kiransu kan albashi ko wasu hakkokinsu ba.

https://p.dw.com/p/55pxP
Gwamna Dauda Lawal Dare na Jihar Zamfara da ke Najeriya
Gwamna Dauda Lawal Dare na Jihar Zamfara da ke NajeriyaHoto: Dauda Lawal/Facebook

'Yan majalisar sun koka da cewa yanzu al'ummar da suka zabe su ba su da wakilci a jihar tun bayan dakatar da su kuma dalilin abin da ya kai su gabatar da bukatun al'ummar ya sa aka dakatar da su kamar yadda dan majalisar da ke wakiltar karamar hukumar Bukuyum ta Arewa Hon. Bashar Abubakar ya tabbatar.

Abin da ya haifar da rikicin majalisar

Sai dai kakakin Majalisar dokokin jihar ta Zamfara Rt. Hon. Ismai'l Moriki ya ce sam ba wannan dalilin ne ya sa aka dakatar da su ba amma dalilin shi ne sun dauki mataki rufe majalisar bayan sun shigar da manufarsu, abin da ya sa doka ta yi aikinta.

Taswirar Jihar Zamfara da ke Najeriya
Taswirar Jihar Zamfara da ke Najeriya

A wani bangaren 'yan majalisar dokokin da aka dakatar sun zargin gwamnatin jihar da ma majalisar dokokin jihar da yin aiki ba bisa doka ba. Hon. Aliyu Ango Kagara dan majalisar da ke wakiltar Talatar mafara ta Kudu ya ce an yi kasafin kudi na shekara ta 2025 da 2026 ba tare da kaso daya cikin uku na 'yan majalisa ba. Kuma babu kudin da aka biya su tun lokacin.

Kakakin majalisar ya ce doka ce sukai amfani da ita wadda ta tanadiduk dan majalisar da aka dakatar ba za a ba shi wani abu ba.Tuni 'yan majalisar da aka dakatar suka je kotu sai dai  Kuma sun kara zargin majalisar da gwamnatin da hada baki da alkalan wajen jinkirta shari'a, abin da majalisar ta musanta.

Majalisar dokokin jihar Zamfara dai nada 'yan majalisu 24 inda yanzu haka guda 15 ne ke aiki sakamakon dakatar da sauran kusan shekaru ga shi kuma ana tunkarar zaben 2027. Shin haka ke nan za a ci gaba da tafiya al'ummar da aka dakatar da 'yan majalisar ba su da wakilci tunda an bukaci 'yan majalisar na su ba da hakuri kafin komawa bakin aiki, sun ki ita kuma majalisar ta ce ba za ta mayar da su ba sai sun ba da hakuri?

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani