Mafita kan matsalar tsaro a Najeriya
July 7, 2021Da alamu dai an kama hanyar kawo karshen tirje-tirje da ma tayar da jijiyar wuya, a kan wannan batu da aka kwashe lokaci mai tsawo ana ja-in-ja a kan halaccinsa ko akasin haka. Za a iya cewa batun na kafa rundunar 'yan sanda ta jihohi a Najeriyar na shirin zuwa karshe, domin kuwa majalisar wakilan kasar ta kai ga yin karatu na biyu a kan wannan kudurin doka da dan majalisa Luke Onofiok ya gabatar domin a halatta samar da 'yan san da na jihohi a Najeriyar.
Ko da ma dai a majalisar dattawan Najeriyar, wannan batu na samar da rundunar 'yan sandan jihohi na samun goyon baya musamman a bangaren 'yan majalisar da suka fito daga yankunan da wannan matsala ta yi Kamari. A karon farko kungiyoyin shiya-shiyya na dattawan arewacin Najeriyar da na Afenifere ta kabila Yarabawa, sun nuna goyon bayansu ga wannan yunkuri domin shawo kan matsalar tsaron. Tun a shekara ta 2019 ne dai, shugaban Najeriyar ya aika da bukatar ga majalisa ta duba wannan batu da ake ci gaba da jan kafa a kansa. Tuni shiyoyin Kudu maso Yammaci da na Kudu maso Gabashi, suka kafa nasu rundunonin tsaron saboda ta'azzara da ma lalacewar halin tsaro a Najeriyar.