1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Boko Haram ta kashe 'yar agaji

Gazali Abdou Tasawa
October 16, 2018

Gwamnatin ta tabbatar da cewa an aiwatar da kisa kan Hauwa Liman ma'aikacciyar kungiyar agajin kasa da kasa

https://p.dw.com/p/36bNO
Hauwa Mohammed Liman
Hoto: Reuters/ICRC

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa Kungiyar Boko Haram ta aiwatar da kisa kan Hauwa Liman ma'aikacciyar nan ta kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross  daya daga cikin jerin ma'aikatan agaji uku da kungiyar ta sace a ranar daya ga watan Maris a lokacin wani farmaki da mayakanta suka kai a birnin Rann da ke a Arewa maso gabashin kasar. 

Ministan yada labarai na kasar ta Najeriya Lai Mohammed wanda ya tabbatar da afkuwar kisan da ya bayyana a matsayin kafirci da rashin imani, ya yi kira ga kungiyar ta Boko Haram da ta sako sauran matan biyu da ke a hannunta da suka hada da wata ma'aikacciyar agaji da kuma wata yarinya 'yar shekaru 15. 

Dama dai a watan Satumban da ya gabata ne kungiyar ta Boko Haram ta aiwatar da kisa kan Saifura Khorsa daya da cikin jami'an agajin uku da ke hannunta inda kuma ta yi barazanar kashe sauran ma'aikatan biyu da ma Leah Sharibu ta makarantar Sikandiren Dapchi da ke a hannunta matsawar dai gwamnatin Najeriya ba ta biya mata bukatunta ba .