Najeriya: Bincike game da yakin Boko Haram
August 11, 2017Talla
Kwamitin wanda ya kunshi wakilai na kungiyoyin farar hula da alkalai da kuma sojojin, zai kai ga bincika zargin da kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi na cewar sojojin Najeriyar sun take hakkin dan Adam a yakin da suke yi da Boko Haram. Tun farko dai rundunar sojojin Najeriyar ta gudanar da irin wannan bincike wanda a kansa ta wanke sojojin daga zargin da ake yi musu na take hakkin jama'a a yakin na Boko Haram