1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci da rashawa a harkar man fetur a Najeriya

Muhammad Bello MNA
April 29, 2019

Wani bincike kan harkar danyan mai da ake wa lakabi da Malabo Oil a Najeriya ya nuna hannun kamfanin Shell da Eni a ciki dumu-dumu.

https://p.dw.com/p/3HfD5
Nigeria Niger Delta Ölverschmutzung Öl
Hoto: Getty Images/C. Hondros

Tun a shekara ta 2011 batun sama da fadi kan cinikin katafariyar rijiyar man nan da aka fi sani da MALABO OIL, da kuma aka samu hannayen shugabannin Najeriya dumu-dumu ciki ya fara bayyana, cinikin kuma da aka nunar an yi matukar sa son zuciya a ciki, ganin yadda kamfunan mai na Shell da Eni da suka sayi rijiyar ta mai, suka gaggauta biyan kudin da ba su taka kara sun karya ba ga kamfanin na MALABO. An dai nunar jami'an Najeriya daga kasa har sama, da suka hada da tsohon shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan, sun amfana daga wannan ciniki da aka yi rufarufa ciki.

To sai dai inda gizo ke sakar a yanzu game da badakalar cinikin wannan rijiya ta mai, a sakamakon wani binciken baya bayan nan da wata kungiya mai zaman kanta mai suna Human And Environmental Development Agenda wato HEDA a takaice ta fidda shi ne cewar, kudaden ma da ake maganar kamfunan na Shell da Eni sun bayar, ba ma daga aljifansu ba ne, face ya fito ne daga ribar kudade da ya kamata Najeriya ta samu na daga hada-hadar wannan mai da kamfunan mai na Shell da Eni ne kawai suka san sirrinta.

Wani tsohon jami'in kamfanin man Shell, Injiniya Ma'azu Magaji ya kara haske kan ainihin abin da wannan kungiya ta HEDA ke san nuna wa duniya.

"Rijiyar mai ce mai dimbin dukiya a cikinta. Da Shell suka gano cewa akwai katafaren arziki a ciki sai suka ce sun yi cinikinta a kan Dala miliyan dubu 1.1. To yanzu wannan kungiya da ta yi bincike ta gano cewa ba wani abu ne wani kaso da za a iya samu daga wannan rijiya. Shi ya sa kungiya ta fito da shi ta ba wa gwamnati don kudin da aka yi ya kai dala miliyan dubu 5.3."

Kamfanin Shell ya share shekaru aru-aru yana aikin hakar mai a Najeriya
Kamfanin Shell ya share shekaru aru-aru yana aikin hakar mai a NajeriyaHoto: DW/A. Kriesch

Wannan rijiyar mai dai da aka nunar na da gangunan danyan mai biliyan tara a kwance a kasa, an sayar wa Shell da Eni ne kan dala biliyan daya da miliyan 300 a shekara ta 2011, wadda kuma sayarwar ko kadan ba ta bisa ka'ida, domin mataki ne na hana wa Najeriya da 'yan Najeriya amfana daga arzikin da zai fito daga wannan rijiya ta mai da ko kadan ba ma ta cikin lissafin jerin rijiyoyin mai da kasar ke hakowa don amfanin 'yan kasa ba.

Mr Olarewaju Surajo shi ne shugaban kungiyar ta HEDA da ta yi aikin bincike na musamman a baya-bayan nan kan badakalar cinikin rijiyar ta mai.

"Kason amfanin da ya kamata Najeriya ta samu na daga wannan arziki na rijiyar mai, wadda aka yi rufa rufa, ya yi baya daga kaso 65 cikin 100 zuwa kaso 41 cikin 100. Koma baya ne matuka wadda kuma ya gaza abin da Asusun Lamuni na Duniya IMF ya shata kan kason da ya kamata kasa ta samu daga cikin duk wata yarjejeniya da za ta shiga kan sarrafa albarkatun kasarta. Abin da ya samu Najeriya abin takaici ne, kuma kan haka kasar ta rasa dala miliyan dubu 1.1. Wannan adadin kudade sh ine aka ba da cin hanci da su maimakon a biya kudaden ga aljifun gwamnati."

Ko da yake wannan alamari na yi wa Najeriya sama da fadi kan arzikinta na mai, da kuma ke gaban kotu wadda kuma ta hada da gaggan mutane na gwamnatocin Marigayi Abacha da ta Dakta Goodluck Jonathan, na ci gaba da daukar hankula.

Ministan shari'a na Najeriya na yanzu Abubakar Malami ya taba bayyana cewar lamarin wannan badakalar da ta hado da gaggan mutane, ana iya sasantawa cikin ruwan sanyi, inda kuma shi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dau matsayin cewar lallai a bincika lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

'Yan Najeriya dai na ci gaba da aza hankulansu kan wannan batu na badakalar rijiyar ta mai, ganin yadda kasar ke matukar bukatar karuwar ayyukan raya kasa.