Najeriya: An saki daruruwan 'yan Boko Haram
February 18, 2018Mutanen dari hudu da saba'in da bakwai na daga cikin mambobin kungiyar dubu daya da aka soma yi wa shari'a a makon jiya a garin Kainji da ke a jahar Naija.
Salihu Othman Isah, wani mai bai wa Atoni Janar na kasar shawara ne ya sanar da sakin mambobin, ya kara da cewa daukar matakin ya zama wajibi bayan da aka gaggara samun gamsassun sheda dake tabbatar da zargin da ake musu na tallafawa ayyukan kungiyar ko kin bayar da bayanai da za su taimakawa masu bincike kan ayyukan kungiyar ba.
Yanzu za'a aika da mutanen jihohinsu inda za a yi ta basu shawarwari kan yadda za su ci gaba da rayuwa cikin sauran al'umma. Shugaban Najeriyan Muhammadu Buhari a baya-bayan nan ya yi ikirarin kawo karshen kungiyar da ta yi sanadiyar rayukan dubban mutane a sanadiyar hare-haren bama bamai.