1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan bindiga sun sace 'yan kallon wasan kwallo 7

Ramatu Garba Baba
January 28, 2019

Wasu 'yan bindiga akalla 20 sanye da kayan sojoji sun yi garkuwa da 'yan kallon wasan kwallon kafa 7 a jahar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3CL6Q
Nigeria Boko Harem Selbstmordattentat WM Public Viewing Damaturu
Hoto: picture-alliance/AP

An yi awon gaba da matasan 7 ne a yayin da suke tsakiyar kallon karawa da aka yi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa ta AC Milan da Napoli a daren ranar Asabar na makon jiya. 'Yan bindigan da ganau ya ce sun kai ashirin, sun far ma garin na birnin Magaji, sanye da kakin soja. Da dama sun yi nasarar tserewa bayan rudanin da suka haifar.

Mai gidan kallon, Sanusi Ishie, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP labarin yin garkuwa da mutanen, ya ce akwai yi yuwar su nemi kudin fansa kafin su saki matasan kamar yadda suka saba yi. Shi ma dai kakakin 'yan sandan jahar Mohammed Shehu, ya tabbatar da labarin inda ya ce sun riga sun baza jami'ansu don kubuto wadanda aka sacen cikin koshin lafiya.

Matsalar tsaro da jahar Zamfara ke fuskanta, ta kasance daya daga cikin manyan kalubale da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke neman wa'adin mulki a karo na biyu ke fuskanta a babban zaben kasar na watan gobe.