Najeriya: An kashe jami′an agaji a Borno | Labarai | DW | 18.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An kashe jami'an agaji a Borno

Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne a Arewa maso Gabashin Najeriya sun kashe mutane hudu a wani harin kwantan bauna a kan ayarin motocin shirin samar da abinci na Majalisa Dinkin Duniya.

'Yan bindigan sun far wa ayarin motocin tirela cike da kayan abinci da sauran kayan agaji da za a kai wa 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita a Kudu maso Yammacin Ngamborun Ngala da ke jihar Borno.

Wasu rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu jami'an hukumar samar da abinci ta duniya wato WFP, tare da yin awon gaba da motocin abincin. Hare-haren 'yan bindiga kan jami'an agaji a arewacin Najeriya ya firgita Majalisar Dinkin Duniya har ta janye ayyukan agaji a yankin a shekarar 2016.

Wannan sabon hari ya zo a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta amince da fidda kudi dala biliyan daya, da zimmar yaki da kungiyar Boko Haram da ke zama barazana ga rayuwar 'yan kasar.