Najeriya: An fasa butun mai mallakin NNPC | Labarai | DW | 10.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An fasa butun mai mallakin NNPC

Tsageru yakin Niger Delta din nan da ake yi wa lakabi da Niger Delta Avengers sun fasa wani bututun mai mallakar kamfanin mai na kasar na NNPC a daren jiya Alhamis.

Masu aiko da rahotanni suka ce an fasa bututun man ne a Sanoki da ke yankin Ogidigben na Warri da ke Jihar Delta da misalin karfe takwas na agogon Najeriya. Mazauna wannan yanki suka ce sun ji wata kara mai karfin gaske lokacin da lamarin ya faru har ma wani basaraken gargajiya Cif Godspower Gbenekama ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar wata gagarumar wuta ta tashi bayan fasa bututun.

A 'yan makonnin da suka gabata dai 'yan kungiyar ta Niger Delta Avengers sun fasa bututan mai da dama yankin na Niger Delta mai arzikin mai na Najeriya a wani mataki da suka ce na yin matsin lamba ga hukumomin kasar na su biya musu bukatunsu.