Najeriya: An amince da na′urar tantance katin zabe | Siyasa | DW | 11.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: An amince da na'urar tantance katin zabe

Hukumar zaben Najeriya ta ba da tabbacin cewar za ta yi amfani da nau'rar tatance katin masu jefa kuri’a a zabe na 2019, amma fa babu batun tattara sakamakon ta hanyar yanar gizo.

Tabbacin da hukumar zaben Najeriyar ta bayar dai ya kara kwantar da hankalin ‘yan Najeriya da dama a game da sanin inda aka kwana a zaben na badi, musamman biyo bayan rashin sanya hannu a dokar zaben kasar da aka yi wa gyaran fuska, wacce a cikinta ne dukkanin wasu sauye-sauye da ma samun hallaci na doka ke ciki. 

Ko da yake ga jam'iyyun adawa na masu dagewa a kan samun dokar zaben ta Najeriya da za ta hallata tattara sakamakon zaben ta hanyar nau'ra mai aiki da kwakwalwa, amma wane tasiri samun haske da tabbaci daga hukumar zabe a kan amfani da katin zai yi dama hallacin hakan. Wani abin da ya fi daukan hankali shi ne yanke shawarar da hukumar zaben ta yi a zaben na badi na cewar ba za’a sake amfani da takardar kadara ba, wacce a kan cika idan nau'ra ta kasa tatance katin jefa kuri’a. A yayin da ake ci gaba da cece-kuce a kan shirye-shiryen zaben na Najeriya da aka sanyawa hukumar zaben ido sosai, amfani da iko na tsara zaben da doka ta bai wa hukumar muhimmi ne a kokuwar da ake na inganta sahihanci zaben fiye da na shekara ta 2015, don kaucewa ci gaba irin na mai ginan rijiya.

Sauti da bidiyo akan labarin