Najeriya: Alakanta sake mayar da ′yan Boko Haram cikin al′umma da rashin tsaro | Siyasa | DW | 17.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Alakanta sake mayar da 'yan Boko Haram cikin al'umma da rashin tsaro

Ana alakanta shirin sake mayar da tsaffin mayakan Boko Haram da aka sakewa tunani cikin al'ummomi da sake dawowar hare-hare da ma tabarbarewar tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojojin ta sake wasu tsoffin mayakan Boko Haram guda 137 da nufin sake mayar da su cikin al'umma don ci gaba da rayuwa. An jima ana alakanta dawowar hare-haren mayakan Boko Haram da sake wasu daga cikin tsoffin mayakan da aka horar da sunan sake musu tunani, abin da yake haifar da fargaba da tsoro na ruruwar wutar wannan rikici.


Ko a baya sai da kungiyar dattawan jihar Borno ta rubuta koke ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya dakatar da wannan shirin na yafewa da sake tunanin tsoffin mayakan Boko Haram wanda suka yi zargin shi ne musabbabin zafafar mayakan Boko Haram a 'yan kwanakin nan.
Wannan dai shi ne ra'ayin mazauna shiyyar da ma masana da masharhanta da suke zargin tsoffin mayakan da sake komawa cikin daji da kuma samar da bayanai na sirri ga 'yan kungiyar.

Yawan hare-haren Boko Haram na tilasta wa mutane gudu daga garuruwansu na asali

Yawan hare-haren Boko Haram na tilasta wa mutane gudu daga garuruwansu na asali


Baana Modu Mainok wani mazaunin daya daga cikin garuruwan da mayakan Boko Haram suka yawaita kai hare-hare da ya tilasta su gudowa zuwa birnin Maiduguri ya tabbatar da wannan zargi da suke yi.

"Gaskiyar al'amari ne akwai tsoffin mayakan Boko Haram wanda an barsu kuma yanzu an zo an kara musu horo an ce za a barsu su saba da mutanen gari, amma mun gansu sun kara komawa wajensu na da. Da zarar mun gansu mu mun sansu da yake tun da mun zauna tare da su tukunna wannan abun ya faru suka shiga jeji kuma sai aka kama su aka kawo su gari, shugaban kasa ya sake su daga baya sai suka kara komawa wajensu na da, shi ya sa muke tsoro muka gudu."

Ana alakanta komawar tsoffin mayakan na Boko Haram zuwa jeji da halin da suka shiga na kyamarsu da ake yi da kuma yadda suka kasa sakewa cikin al'umma saboda tsangwama. Daya daga cikinsu tsoffin mayakan ya tabbatar da halin da ya sa wasu daga cikinsu ke komawa cikin jeji don sake hadewa da 'yan uwansu bisa sharadin za a sakaye sunanshi.

"Muna samun matsala ta wajen mutane yadda suke nuna mana irin tsangwama kamar mu ba mutane ba ne. Yanzu haka akwai mutanenmu amma sun koma jeji saboda kunci da yunwa da wahalhalu da suke sha."


Nan dai wata cibiyar canja tunanin mayakan Boko Haram ne da ke jihar Gombe

Nan dai wata cibiyar canja tunanin mayakan Boko Haram ne da ke jihar Gombe

Yawancin al'umma dai na ganin shirin sake tarbiyar tsoffin mayakan na Boko Haram na bukatar gyara da fasali, saboda haka suka nemi a sakewa shirin tsari domin ganin ya samu nasarar da ake nema. Malam Adamu Dan Borno wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya.

"Gaskiya gwamnati ta yi kuskure ta yadda ba ta gamsu cewa su ma tunanin nasu ya canza ba. Ya kamata a dawo a yi waiwaye a rika neman hanyoyi, a rika neman wadanda suka san me suke yi, su rika bai wa gwamnati shawarwari a kan irin lamari na Boko Haram."
Shi ma Mu'azu Abubakar Sadiq na kungiyoyin fararen hula na ganin shirin na bukatar sake masa fasali musamman saboda yadda ake samun matsaloli da al'ummomin da suka koma a cikinsu.


"Ba soja ba ne kadai za mu sa wannan sauyin hali da ake sa musu, ya kamata a nemi shawarwari na al'umma, al'umma yaya kuke gani ake son a yi wa wadannan mutanen? Kuna ga akwai wani wuri kafin a kawo su wurinku? Duk wannan abin ya kamata a ji daga bakin al'umma, a ji a bakin sarakuna, a ji a bakin matasa, a ji a bakin matan kasuwa, ta yaya suke so a canza sauyin halin ga wadanda suka kawo wadannan matsaloli."

Kokarin da wakilinmu a Maiduguri Al-Amin Suleiman Muhammad ya yi na ji daga jami'an tsaro domin sanin ko suna sane da cewa mayakan na komawa jeji da ma zargin da al'umma ke yi na ruruwar wannan rikicin saboda tsoffin mayakan, ya ci tura.
Amma a baya Manjo-Janar Bamidele Mathew Shafa shugaban shirin gyara dabi'un tsoffin mayakan Boko Haram ya bayyana cewa ba su samu labarin na tsangwamar ko daya daga cikin wadanda suka mayar cikin al'umma ba.

Sauti da bidiyo akan labarin