Mutuwar bakin haure a teku | Labarai | DW | 29.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutuwar bakin haure a teku

Sama da bakin haure 3,000 ne kawo yanzu suka hallaka a tekun Mediterranean a kokarin da suke na shigowa nahiyar Turai ta ko wacce hanya.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa IOM ce ta bayyana hakan a rahoton da ta fitar a Litinin din nan inda ta ce adadin ya ninka na shekara ta 2011. Nahiyar Turai dai na fuskantar kwararar bakin haure mafi yawansu daga yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yankin arewacin Afirka da ke fama da rikici, abun da ke zama wani babban kalubale ga nahiyar baki daya. Wannan rahoto na IOM dai na zuwa ne mako guda bayan da wani jirgin ruwa makare da bakin haure 500 daga kasashen Siriya da Palasdinu da kuma Masar ya nutse, inda aka kiyasta cewa akwai kannan yara 100 daga cikin wadanda suka nutse a hadarin da aka bayyana da mafi muni a wannan shekara. Mutane 11 da aka gano da ransu sun bayyana cewa wadanda sukai yo safararsu ne suka haddasa hadarin da ya afku a kusa da gabar tekun Malta.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu