Mutum 28 sun mutu a hadarin mota | Labarai | DW | 28.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutum 28 sun mutu a hadarin mota

Rahotannin daga Nijar na cewa wasu mutane akalla 28 sun salwanta a sakamakon wani hadarin mota da ya auku a wannan Asabar a hanyar Dosso.

Akwai wasu mutane takwas da ke cikin mawuyacin hali a sanadiyar hadarin na yau, sanarwar daga hukumomin kasar na cewa akasarin fasinjojin da ke cikin motocin ukun da suka yi karo da juna, kirar bas, sun taso ne daga Najeriya da ke makwabtaka da kasar ta Nijar.