1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane na kara shiga kunci a Ukraine

November 27, 2022

Yayin da ake ci gaba da fama da daukewar wutar lantarki sakamakon hare-haren Rasha a Ukraine, kasar za ta ci gaba da fuskantar sanyin hunturu mai tsananin gaske.

https://p.dw.com/p/4K96V
Birnin Kyiv na kasar Ukraine cikin dusar kankara
Birnin Kyiv na kasar Ukraine cikin dusar kankaraHoto: Jeff J Mitchell/Getty Images

Birnin Kyiv da ke fadar gwamnatin kasar Ukraine zai kara shiga cikin yanayi mai tsananin sanyi, inda ake sa ran dusar kankara za ta mamaye ko'ina.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da miliyoyin 'yan kasar ke fama da rashin wutar lantarki da ke hana su samun amfani da na'urorin dumama gidaje da sauran wurare.

Kamfanin samar da wutar lantarki a kasar ta fada a ranar Asabar cewa, kashi daya bisa hudu ne kadai ke samun wuta yanzu a Ukraine, sannan kuma za a dauki lokaci cikin matsalar.

Shugaba Volodymyr Zelenskiy, ya ce ana daukar matakan takaita amfani da lantarki cikin yankuna 14 daga cikin 27 da ake da su, abin da ke shafar sama da mutum dubu 100 na kowane yanki da ake fama da karancin makamashin.

Hare-haren da Rasha ta kaddamar kan tashoshin samar da lantarki a Larabar da ta gabata ne dai, suka kara ta'azzara lamura a kasar.

Karancin wutar dai ta haddasa rashin ruwan sha mai tsafta da al'uma ke bukatar a kasar ta Ukraine.