Mutane dubu 15 sun gudu daga jihar Borno | Labarai | DW | 22.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane dubu 15 sun gudu daga jihar Borno

Hukumar NEMA ce ta bayar da adadin mutane da suka kaurace wa matsuguna bayan hare-haren 'yan Boko Haram a Damboa da wasu garuruwa na jihar Bornon Najeriya.

Hukumar bada agajin gaggawa ta tarayyar Najeriya wato NEMA ta bayyana cewa sama da mutane dubu 15 ne suka kaurace wa matsugunansu, bayan wasu jerin hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a karshen mako a jihar Borno. Mutane gwamai ne dai masu gaggwarmaya da makaman suka kashe a garin Damboa tare da kona gidaje da dama yayin da suka kutsa garuruwa shida na jihar Borno.

Yanzu haka dubban mutane da ke cikin mawuyacin hali suke neman mafaka a garin Biu na jihar Borno, yayin da wasu kuma suka tsere zuwa wasu jihohin ciki kuwa har da Gombe.

Rahotanni sun nunar da cewa 'yan Boko Haram ne ke rike da ikon yankin Arewaci da kuma tsakiyar jihar Borno duk da barazanar da gwamnatin ta yi na amfani da karfi domin fatattakarsu daga yankin. Bayan ma garin Damboa, 'yan Boko Haram sun kafa tutoci a wasu sassan Borno tare da kafa shingayen bincike na ababen hawa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Suleiman Babayo