Mutane da dama sun rasu a hare-haren Iraki | Labarai | DW | 13.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun rasu a hare-haren Iraki

Wasu jerin hare-haren na bam da aka kai har sau uku sun yi sanadiyyar rasuwar mutane 25 a wasu yankunan Bagadaza wanda galibin mazaunansu mabiya tafarkin Shi'a ne.

Jami'an 'yan sandan suka ce biyu daga cikin hare-haren na kunar bakin wake ne kuma an kai su ne a birin Sadr yayin da aka kai cikon na ukun birnin Kadhimiyah lokacin da ake gudanar da shagulgulan bikin sallah da suka yi wa lakabi da Eid al-Ghadir.

Ma'aikatar cikin gidan Irakin da ta tabbatar da wannan labarin ta ce baya ga wanda suka rasu, da dama sun samu raunuka wasunsu ma munana kuma hare-haren sun wakana ne lokacin da jama'a ke tsaka da gudanar da harkokinsu.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance ko wacce kungiya ce ta kai wannan hare-hare ba ko ma dalilin yin hakan.