Mutane biyu suka rasa rayukansu a rikicin zabe a Congo | Labarai | DW | 30.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane biyu suka rasa rayukansu a rikicin zabe a Congo

Jamian zabe guda biyu ne aka kashe a JDC,adaya daga cikin rigingimun da suka barke ayayin gudanar da zagaye na biyun zaben shugaban kasa a jiya Lahadi,sakamakon zaben da zaa sanar cikin makonni 3 masu gabatowa.Rahotanni daga birnin Kinshasa na nuni dacewa jamian biyu,sun gamu da ajalinsu ne da asubahin yau,a ganin Bunia dake gunduwar Ituri,wanda ke yankin arewa maso gabashin kasar.Tuni dai aka cafke jamiin sojin daya kashe jamian,kana zaa cigaba da gudanar da bincike akansa.Wannan kisan gilla da akayiwa jamian zaben Congon dai,ya haifar da tashe tashen hankula tsakanin alummomin yankin,dasu ka jima cikin rikicin sojojin dana mayakan sakai.