Mutane 34 sun mutu a hamadar kasar Nijar | Labarai | DW | 16.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 34 sun mutu a hamadar kasar Nijar

An gano gawawakin wasu mutane 34 cikinsu yara kanana 20 a cikin dajin Sahara na Arewacin kasar Nijar iyaka da Algeriya.

Niger Agadez Sahara Flüchtlinge

Wata mota dauke da 'yan Ci-rani a Agadez

Wata majiyar tsaro ta sanar wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP cewa, mutanen da suka hada da maza biyar, mata guda tara, da kuma kananan yara 20, an same su ne kusa da garin Assamaka da ke a matsayin mashiga ta kan iyakar kasar ta Nijar da makwabciyarta Algeriya.

Masu yi musu jagora ne dai suka gudu suka bar su a tsakanin ranekun shida zuwa 12 ga watan nan a cewar sanarwar, wadda ta ce gawawakin mutun biyu kawai aka iya tantance wa da suka hada da wani dan Najeriya, da kuma wata mata 'yar Nijar mai shekaru 26 da haihuwa inda ake sa ran kishirwa ce ta hallakasu. Kasar ta Algeriya dai ta zamanto wani wurin da 'yan cirani ke zuwa, tun bayan da harkoki suka tabarbare a kasar Libiya.