Mutane 20 sun mutu a wani hari a Iraki
July 19, 2013Talla
Jami'an 'yan sanda da ke Bakuba a birnin na Bagadazan wanda su ka tabbatar da kai harin sun ce baya ga asarar rayukan da aka samu a harin, wasu mutane arba'in sun jikkata.
Yankin na Bakuba da aka kai wannan hari na yau dai ya sha fama da hare-hare irin wadannan domin ko a ranar Talatar da ta gabata sai da aka kai hari kan mabiya tafarkin na Sunna a wani masallaci da ke Muqdadiyah inda mutane sha biyar su ka ce ga garinku nan.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin na yau, sai dai hukumomi sun ce su na ta yin bakin kokarinsu wajen bankado wadanda ke da hannu domin gurfanar da su gaban kuliya.
Mawallafi. Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe