Mutane 20 suka mutu a wani rikicin kasar Kamaru | Labarai | DW | 24.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 20 suka mutu a wani rikicin kasar Kamaru

Wani sabon tashin hankali a kan iyakar Najeriya da Kamarun ya yi sanadiyar mutuwar mutane da kwana gidaje

Rikicin dai ya samo asali bayan wani tashin hankali tsakanin wasu da ake kyautata zaton makiyaya ne da suka gujewa rikicn Boko Haram a Najeriya suka tsallako cikin Kamarun. A cewar wani dan majalisar dokokin kasar ta Kamrun, rikicin ya barke ne bayan wasu da ake tsammanin makiyaya ne, suka kosa da irin matsin lamba da suke samu wajen kauyawan da ke kusa da inda suka yada zango domin neman wurin kiwo. Ya ce 'yan kauyen sun bukaci da makiyayan su tashi daga yankin, abinda ya haddasa fadan kuma an kona gidaje da dama. Yanzu haka dai rahotanni suka ce mazauna kauyukan da dama sun tsere, kuma an bayyana cewa daga cikin karin mutanen da suka jikkata, harda wasu sojojin Kamarun wadanda suka kawo dauki daga bisani.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Pinado Abdu Waba