1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musayar fursunoni sama da 40

Zainab Mohammed Abubakar
January 11, 2023

Rasha da Ukraine sun amince da wani sabon shirin musayar fursunoni a tattaunawar da ba kasafai ake yi ba a Turkiyya, tare da tattauna samar da hanyar aiyukan jin kai.

https://p.dw.com/p/4M2KT
Russland-Ukraine-Krieg | Kiew
Hoto: Aris Messinis/AFP

 Jami'in kare hakkin bil'adama na Ukraine Dmytro Lubinets ya gana da takwararsa ta Rasha Tatyana Moskalkova a gefen taron kasa da kasa da ake yi a birnin Ankara wanda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya halarta.

Moskalkova ta shaidawa manema labarai bayan taron cewa, sun amince da musayar fiye da fursunoni 40 daga kowane bangare. Sai dai Mr Lubinets na Ukraine bai ambaci wani adadi ba a cikin jawabinsa ga manema labarai bayan tattaunawar sa'o'i uku.

Ana sa ran jami'an kare hakkin bil'adaman biyu za su yi musayar jerin sunayen fursunonin da duk wata yarjejeniyar da za a yi, a wani taron a gobe Alhamis. Matakin da ke zuwa duk da fadan da ya barke a tsakaninsu tsawon watanni 11 da suka gabata.