Muna kakkabe Boko Haram daga tungarsu-Rundunar Najeriya | Siyasa | DW | 11.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Muna kakkabe Boko Haram daga tungarsu-Rundunar Najeriya

Baya ga cafke mayakan Boko Haram, rundunar sojan Najeriya ta ce tana kuma samun galaba wajen fatattakarsu daga sansaninsu.

Babban kwamandan rundunar da ke yaki da kungiyar Boko Haram wanda ake yi wa lakabi da "Operation Lafiya Dole" Manjo Janar Lucky Irabo ya sanar da cewa rundunar ta samu nasarar cafke mayakan Boko Haram guda 963 tare da ci gaba da kakkabe 'yan kungiyar daga shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.


A wata ganawa da manema labarai da yammacin ranar Laraba Manjo Janar Lucky Irabo ya ce daga cikin wadanda aka samu nasarar cafkewa har da Amir wato daya daga cikin jagororin kungiyar da kuma likita mai kula da lafiyar mayakan kungiyar.
Sauran wadanda rundunar ta ce ta kame har da matan mayakan kungiyar da 'ya'yansu, inda wasu guda biyu kuma suka mika wuya da kuma makamansu don kashin kai. Rundunar ta kuma ce yanzu haka ta karbe iko da dukkanin yankunan da ke kan iyakokin Najeriya da Kamaru da kuma Chadi gami da iyakokin Nijar, inda dakarun take ci gaba da farautar mayakan Kungiyar.

Samun bayanai masu muhimmanci


Ko da aka tambaye shi kan ko matan da aka kame sun bayyana maboyar mazajensu Janar Irabo ya ce:
"Muna kan bincike don haka lokacin bai yi da za mu bayyana wa manema labarai abubuwan da wadannan mata suka shaida mana, amma zan baku tabbacin cewa dukkaninsu suna bamu bayanai masu gamsarwa da zai iya kai ga gane wadanda suke tallafa wa ayyukan Boko Haram."


Boko Haram (Java)

Da yawa daga cikin mayakan Boko Haram sun ajiye makamansu

Yanzu haka kuma rundunar ta fadada ayyukanta zuwa bakin tafkin Chadi saboda yadda yankin yake da hadari kamar yadda Janar Irabo ya bayyana.


"Tafkin Chadi ya kasance mai matukar matsala saboda yadda yanayin wurin yake, shi ne dalilin jibge dakarun ruwa a yankin kuma an samar musu da kayan aiki domin tallafa wa sojojin hadaka da ke taron dangi a daya bangaren."


Rundunar ta sanar da hallaka mayakan Boko Haram da dama da ke kokarin kai hari ko kuma neman hadewa da 'yan uwansu, inda ko a ranar Talata da dare 'yan kungiyar sun kai hari kan sojojin Najeriya, inda sojojin suka hallaka 'yan kungiyar da dama a yankin Marte. Sai dai soja daya ya mutu wasu hudu kuma sun jikkata.


A cewar Malam Ibrahim daya daga cikin 'yan jarida da suka halarci taron manema labara "irin yadda sojojin ke bayyana abinda ke faruwa da kansu ya nuna cewa yanzu kan ana yin yaki da gaske."

 
Sai dai irin yadda sojojin ke bayyana cewa ana kai musu hare-hare tare da yi musu kwantan bauna wanda ke kaiwa ga hallaka sojojin, masharhanta na ganin har yanzu da sauran aiki tun da ba za a kai ga gano masu daukar nauyin ayyukan kungiyar ba inda suka nemi a maida hankali a kai in dai ana son cimma nasarar da ake nema.

Sauti da bidiyo akan labarin