Mummunan harin bam a Kano | Siyasa | DW | 30.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mummunan harin bam a Kano

Mutane da yawa ne suka rasa rayukansu a tashin bama-bamai guga hudu a birnin na Kano bayan watanni da sararawar irin wadannan hare-hare.

A daren ranar Litinin ne wasu bama-bamai da suka tashi a unguwar Sabon Garin Kano suka haddasa rasuwar mutane da dama bayan wasu da suka jikkata. Rahotanni sun tabbatar da cewar zuwa ranar Talata da rana akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu. An dai dauki tsawon lokaci a jihar Kano ba tare da samun wani tashin hankali ba. Wannan hari dai yayi kama da wanda kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram ke kaiwa, ko da yake har zuwa wannan lokaci babu kungiyar da ta ayyana daukar alhakin kai harin.

Tun da misalin karfe tara na daren ranar Litinin ne aka fara jiyo karar fashewar wani abu mai kara da ake kyautata zaton bam ne a unguwar New Road dake Sabon Garin, daga bisani kuma aka sake jiyo wata karar mai karfi wadda daga bisani aka tabbatar da cewar wasu bama-baman ne suka sake tashi a unguwar Enugu Road dake wannan yanki na Sabon Gari.

Sau hudu aka ji karar tashin bam

Wasu da suka shaida wannan al'amari sun bayyana cewar sau hudu ana jiyo karar fashewar wadannan bama-bamai, wadanda suka haddasa rasuwar mutane da dama baya ga wasu da suka jikkata.

A residents peers through the shattered widow of a badly-damaged car at the scene of an explosion targeting an open-air beer garden at Enugu Road in the downtown Sabon Gari neighbourhood of the city on July 30, 2013 in Kano. The death toll from a series of bomb blasts that rocked a mainly Christian area of northern Nigeria's largest city of Kano late on July 29 has risen to 12, the military said today, blaming Islamist group Boko Haram for the attacks. The statement blamed the attack on suspected Boko Haram members and said packages that caused the explosions were left in the mainly Christian Sabon Gari area of Kano. AFP PHOTO / AMINU ABUBAKAR (Photo credit should read AMINU ABUBAKAR/AFP/Getty Images) Erstellt am: 30 Jul 2013 Editorial-Bild-Nummer: 175046207 Beschränkungen: Bei kommerzieller Verwendung sowie für verkaufsfördernde Zwecke kontaktieren Sie bitte Ihr lokales Büro. Vollständige redaktionelle Rechte in Großbritannien, USA, Irland, Italien, Spanien, Kanada (außer Quebec). Eingeschränkte redaktionelle Rechte in allen anderen Ländern. Wenden Sie sich bitte an Ihr lokales Büro. Lizenztyp: Lizenzpflichtig Fotograf: AFP/Freier Fotograf Kollektion: AFP Bildnachweis: AFP/Getty Images Max. Dateigröße/ Abmessungen/ dpi: 12,1 MB - 2371 x 1778 Pixel (83,64 x 62,72 cm) - 72 dpi Die Dateigröße für den Download weicht u. U. von den Angaben ab. Quelle: AFP Releaseangaben: Kein Release verfügbar. Weitere Informationen Strichcode: AFP Objektname: Par7627280 Urheberrecht: 2013 AFP Suchbegriffe: Stadt, Zerbrochen, Konflikt, Horizontal, Im Freien, Wohnviertel, Bier, Nigeria, Sehen, Explodieren, Auto, Gewalt, Stadtzentrum, Witwe, Angriff mit Bombe, Eigenheim, Kano - Nigeria, Terrorismus.

Daya daag cikin motocin da suka ragargaje sakamakon harin

Jim kadan bayan faruwar harin ne jami'an tsaro suka ringa diban gawarwaki da wadanda suka jikkata zuwa asibitocin dake jihar ta Kano. Asibitin Murtala shi ne babban asibitin da aka fi kai wadanda harin ya rutsa da su, ya kasance cike da gawarwaki da kuma wadanda suka jikkata.

Garzawa asibiti don neman karin bayani

Wani matashi dake cikin rukunin wadanda suka je domin duba 'yan uwansu ya bayyana cewar harin ya rutsa da dan uwansa ko da yake dai bai rasa ransa ba amma ya jikkata.

Basiru Iliyasu magidanci ne da shi ma ke rukunin wadanda suka halarci asibitin domin ganin abin da ya faru, yayi harin haske a kan abin da ya gani da cewa bai taba ganin mummunan abu na rashin imani irin wannan ba.

A nata bangaren rundunar sojin Najeriya a jihar Kano ta tabbatar da faruwar harin ta bakin kakakin ta Captain Ikedechi Iweaha, sai dai bai yi wani karin haske ba.

Mawallafi: Nasir Salisu Zango
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin