Mulkin kaka-gida a nahiyar Afirka | Siyasa | DW | 11.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mulkin kaka-gida a nahiyar Afirka

Wasu masu mulki a nahiyar Afirka suna ci gaba da kaka-gida da mamaye komai tare da neman mayar da mulki siyasa zuwa gado daga iyaye zuwa 'ya'ya.

Faure Essozimna Gnassingbe Eyadema | Mahamat Idriss Deby | Joseph Kabila | Ali Bongo Ondimba

Faure Essozimna Gnassingbe Eyadema shugaban Togo, Mahamat Idriss Deby shugaban Chadi, Joseph Kabila tsohon shugaban Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, Ali Bongo Ondimba shugaban Gabon

Mulkin gado a Afirka da ke ci gaba da samun wurin zama na takaita mulki hannun wasu tsurarun al'umma wanda hakan ke hana a dama da wasu cikin sha'anin mulki. Misalai karara da ake gani a kasashen Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da Togo da Chadi da kuma Gabon. Batun da ake ganin shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu na son dan shi Thiik Mayardit ya gaji kujerarsa a babban zaben kasar da za a gudanar a fadi. Masana dai na ganin hakan a matsayin wata babbar barazana ga dimukaradiyya.

Mulkin gado ba sabon abu ba ne yanzu a duniya, wanda ke ba da dama ga ahalin gida daya su yi mulkin karba-karba da kuma rike madafun ikon kasa na tsawon lokaci, batun da masana ke gargadi a kai da tuni ya fara zama ruwan dare a nahiyar Afirka kuma suek ganin hakan na takaita mulki a hannun wasu tsurarun mutane. A ra'ayin masana irinsu Dr Alidu Seidu na sashin kimiyar siyasa a jami'ar kasar Ghana yana ganin al'adu sun yi tasiri wajen tabbatuwar siyasar gado a nahiyar.

Chadi | Mahamat Idriss Déby, shugaban gwamnatin wucin gadi ta soja (CMT)

Shugaba Mahamat Idriss Déby na Chadi

Sai dai kuma mai sharhi kan lamuran da suka shafi siyasa a kasar Kenya Martin Adat ya baiyana wa DW cewa mulkin gado ba zai ta amfanin nahiyar ta kowace fuska ba.

A lokuta da dama dai shugabanin Afirka na horas da 'yan uwansu don su gaje su ba tare da bin ka'idojin ba, wanda hakan ke haifar da rudanin da hargitsin siyasa. Alidu ya ce ana gudanar da siyasar a kasashen yamma cike ne da gasa , inda ake fifita cancanta fiye da 'yan uwantaka. Martin Adat kuwa na da yakinin cewa shugabanin Afirka ba su da sha'awar baje wa a faifai saboda irin muradun na kashin kai da suke da shi.

Ana dai ganin shugabanin na fargabar girban abun da suka shuka ne bayan sauka daga kan mulki, a don haka ne ake gudanar da siyasar gado cikin rashin gaskiya inda talakawa ke dandana kudarsu. A nahiyar Afirka, babu wata doka da aka tanadar da za ta hana aiwatar don hana wani ya gaji mulkin dan uwansa, a don haka 'yan kasar ne kawai ke da ikon kawo karshen wannan akida.

Masana dai na ganin matakin nuna kin amincewa da hakan shi ne daukar matakin shari'a da kuma gudanar da zanga-zanga, wanda suke fatan nan bada jimawa al'ummar kasashen su samu fahimta sosai kan illar wannan mulkin gado ga sha'anin mulki da kuma ci-gaban kasarsu.

Sauti da bidiyo akan labarin