Muhawarar manyan jam′iyyun Jamus | Labarai | DW | 24.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Muhawarar manyan jam'iyyun Jamus

Angela Merkel ta CDU da Martin Schulz na SPD da sauran shugabannin manyan jam'iyyu sun yi musayar zafafan kalamai a wata muhawara da aka yi bayan fidda hasashe na farko na sakamakon zaben da aka yi.

Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran manyan jam'iyyun kasar sun yi wata tattaunawa ta talabijin bayan fitar hasashe na farko na sakamakon zabe inda muhawarar ta kasance mai zafi bisa ga irin kalaman da suka rika fita daga bakin shugabannin manyan jam'iyyun. Shugaban SPD Martin Schulz a lokacin muhawarar ya zargi Merkel da baiwa 'yan jam'iyyar AfD dama ta shiga majalisa saboda irin salonta na yakin neman zabe da kuma kauracewa muhawara gabannin zabe.

Deutschland Bundestagswahl | Elefantenrunde (picture-alliance/dpa/G. Breloer)

Merkel da Schulz sun yi musayar kalamai masu zafi yayin muhawarar da aka yi

Schulz har wa ya ya ja kunnen jam'iyar Greens mai rajin kare muhalli da kuma FDP mai sassaucin ra'ayi wanda ake tunanin za su iya kawance da CDU ta Merkel kan su yi taka-tsantsan game da wannan batu domin a cewarsa Merkel za iya yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta cigaba da kasancewa kan madafun iko sai dai Merkel ta maida masa martani inda ta ke cewar ''yanzu ana lokaci ne mai cike da sarkakiya don haka ya kamata kowacce jam'iyya ta maida hankali wajen yin abinda ya dace''.

Shugabar ta gwamnatin Jamus ta ce ita kam yanzu kofarta a bude ta ke ga jam'iyyar da ke sha'awar yin kawance da ita ciki kuwa har da SPD duk kuwa da cewar jam'iyyar ta ce za ta kasance ne a matsayi na 'yar adawa a majalisa. To sai dai duk da irin mika goron gayyata da Merkel ta yi ga jam'iyyu na su zo a kafa gwamnati, a baya CDU ta sha nanatawa cewar ba ZA ta yi kawance da jam'iyyar AfD ba. AfD din dai na zaman jam'iyya mai kyamar baki kuma ita ce kan gaba wajen adawa da shirin Merkel na karbar 'yan gudun hijira don bayan bayyana nasara da ta samu ta shiga majalisa, jam'iyyar ta ce za ta nemi a kafa wani kwamiti da zai binciki Merkel kan shirinta na karbar 'yan gudun hijira.