Mugabe ya fara sabon wa′adin mulki | Siyasa | DW | 22.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mugabe ya fara sabon wa'adin mulki

Bayan da ya lashe zaben shugaban kasar Zimbabwe da ake takaddama kai, an rantsar da Robert Mugabe a wani sabon wa'adin mulki na shekaru biyar.

Kamar yadda ya saba a jawabansa, Mugabe mai shekaru 89 da kuma zai yi wa'adi na bakwai a jere, yayi suka da kakkausan lafazi ga kasashen yamma da ke masa kallon dan kama karya da ma dai kasashen da ke zarginsa da tafka magudi yayin zaben da suka fafata da tsohon Firaminista kuma dan jam'iyar adawa ta MDC, Morgan Tsavangirai.

DW.COM