Kalubalen samar da wanda zai gaji Mugabe | Siyasa | DW | 22.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen samar da wanda zai gaji Mugabe

Robert Mugabe ya yi rantsuwar fara aiki karo na bakwai tun bayan da ya dare kan kujerar mulkin Zimbabwe. Sai dai an fara nuna fargaba kan halin da kasar za ta shiga idan ya mutu ba tare da sanar da sunan magajinsa ba.

Babu dai wani mahaluki da ya san wanda zai gaji Robert Mugabe idan wa'adinsa na mulki ya cika ko kuma ya yi murabus ko ma dai ta Allah ta kasance. Ko da a lokacin da manaima labarai suka yi ma sa tambaya game da wannan batu a ranar da aka gudanar da zaben gama gari a Zimbabwe, sai dai shugaban da ya fi takwarorinsa na kasashen Afirka yawan shekaru ya fusata tare da nuna alamun gudanar da salon mulkin mutu ka raba.

" Mene ne dalilan da ba a son ganin na kammala wa'adina na mulki? Mene ne amfanin tsayawa takara idan domin in yi murabus ne daga bisani?"

Simbabwe Wahlen Unterstützer Robert Mugabe

Jam'Iyyar ZANU-PF na da karfin fada a ji a Zimbabwe

Shi dai Robert Mugabe mai shekaru 89 da haihuwa ya shafe shekaru 33 a kan karagar mulkin Zimababwe. Ko da ya ke dai ba shi da wata tartibiyar cuta da ke damunshi, amma kuma da yawa daga 'yan kasarsa na dasa ayar tambaya game da makomar Zimbabwe idan Mugane ya kau. Ya zuwa yanzu dai bai taba dago batun wanda zai maye gurbinsa ba idan ya sauka don radin kansa ko kuma ya kamu da wata mummunar cuta. Saboda haka ne ma Wilf Mbanga, edita a jaridar Zimbabwean Newspaper a London ke cewa ba karamin rudani za a fuskanta ba a jam'iyyar ZANU-PF da ke mulki idan shugaba Mugabe ya mutu ko kuma ya kasa tafiyar da harkokin mulki ba.

"Shi ne kashin bayan gaba dayan jam'iyyar. Idan Mugabe ya mutu a gobe, lallai rikici ne zai barke a cikin jam'iyyar ZANU-PF. Mugabe ne kawai zai iya dinke baraka tsakanin 'yayan jam'iyar da ba sa jituwa da juna."

Mataimakiyar shugaban kasa ce za ta gaji Mugabe?

Ba wasu ba ne ke jagorantar bangarorin biyu da ke gaba da juna ba, illa wadanda ake sa ran za su iya gadan kujerar mulkin Robert Mugabe. Na farko dai shi ne ministan tsaro Emmerson Mnangagwa, wanda ya taba rike mukamai da dama a cikin gwamnati ciku kuwa har da kakakin majalisa. Sai dai a shekara ta 2004 ya yi asarar mukaminsa na sakataren ZANU-PF da ke jan ragamar mulkin Zimbabwe, saboda abin da masharhanta harkokin siyasa sun danganta da karfin fada a ji da ya samu a cikin jam'iyar. Mutum na biyu da ke nuna maitarsa a fili akan shugabancin kasar Zimbabwe ita ce mataimakiyar shugaban kasa Joice Mujuru, wace ta fi samun karbuwa a halin yanzu. Ga ma abin da Thomas Deve ke fada game da Mujuru.

Richard Tsvangirai Ministerpräsident Simbabwe

So uku Tsvangirai ya sha kaye a hannun Mugabe

"Babu shakka cewa ta su ta zo daya da mataimakiyar shugaban kasa Joice Mujuru. Akwai lokacin da ta yi murabus daga gwamnati. Amma kuma Mugabe ya mika ma ta hannu tare da tararta hannu biy-biyu. Idan ku ka lura da yadda ta ke tafiyar da harkokin mulki, za ku gane cewa babu shakka ta na da babban gurbi a jam'iyya."

Jam'iyyar MDC ta Tsvangirai ta rasa farin jinita

Ko ma dai wa jam'iyyar ZANU-PF za ta tsayar a matsayin wanda zai gaji Mugabe, zai zame wa madugun 'yan adawa kasar Morgan Tsvangirai wani babban kalubale. So uku tsohon firaministan ya fafata da shugaba Robert Mugabe a zaben shugaban kasa ba tare da samn nasara ba. Da yawa daga cikin magoya bayan jam'iyarsa ta MDC ba su gani a kasa ba bayan da Tsvangirai ya shiga aka dama da shi a cikin gwamnatin hadin kan kasa. saboda haka ne suka fice daga MDC tare da kafa wata sabuwar jam'iyya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin