Takaddama a kan ranar zabe a Zimbabwe | Siyasa | DW | 20.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama a kan ranar zabe a Zimbabwe

Al'ummar kasar Zimbabwe na zaman jiran sabuwar ranar da za a sanar, domin gudanar da babban zaben kasar da 'yan adawa ke neman a dage da watanni uku.

Kotun Tsarin Mulki a Zimbabwe ta bayyana cewa ta karbi korafi da ke bukatar a dage ranar gudanar da zabe a kasar da makwanni biyu daga fadar gwamnati a karakshin jagorancin Shugaba Robert Mugabe. Wannan batu dai ya zo ne a lokacin da Firamininstan kasar ke cewa a dage zaben zuwa watan Oktoba mai zuwa.

Tun a karshen mako ne kungiyar hadin kan yankin kudancin Afirka da aka fi sani da SADC ta bukaci a jinkirta gudanar da zaben 'yan majalisa da kuma na shugaban kasa a Zimbabwe har zuwa wani lokaci, wanda hakan ya sanya Mugabe ya mika bukatar dage zaben ga Kotun Tsarin Mulkin kasar wadda ita ce ta bukaci a gudanar da zaben kafin karshen watan Yuli mai zuwa tun da farko.

Zimbabwe Wahlen Morgan Tsvangirai 13.06.2013

Firaministan Zimbabwe Morgan Tsvangirai

Sai dai kuma madugun 'yan adawar kasar Morgan Tsvangirai ya bukaci a fara yi wa dokokin da suka shafi 'yancin fadar albarkacin baki da kuma na tsaro gyaran fuska kafin a gudanar da zabukan. Tsvangirai dai shine Firaministan kasar a yanzu haka karkashin jagorancin gwamnatin hadin gwiwa da aka shafe shekaru hudu ana gudanarwa tsakaninsa da Shugaba Mugabe, kuma ya bukaci da a dage zaben har zuwa watan Oktobar wannan shekara da muke ciki.

Ministan kudi na Zimbabwe kuma babban jami'i a jam'iyyar Firaminista Tsvangirai ta MDC Tendai Biti, ya yi karin haske kan dalilansu na bukatar a dage zaben da watanni uku. Ya ce "akwai matsaloli guda hudu da suka tunkaro mu, na farko matsalar shari'a, daukar matakin da ya sabawa shari'a ta hanyar fakewa da hukuncin kotu, na biyu yadda za a gudanar da zaben, na uku matsalar kudi, na hudu kuwa shine yadda za a gudanar da zabe da al'umma za su amince da shi".

Al'ummar Zimbabwe dai na da mabanbantan ra'ayoyi kan batun gudanar da zaben kasar da ake takaddama a kansa, kamar yadda wasu suka bayyana na su ra'ayin. Ya ce" A tunanina a matsayina na matashi dan Zimbabwe, a shirye muke mu je mu kada kuri'a, ko da ba za a samu gyara a bangaren 'yancin fadar albarkacin baki da kuma fannin tsaro ba, saboda wasu jamiyun siyasa sun ki amincewa a samu gyaran". Ita kuwa wannan cewa take " Ban da mu ayi zabe a Zimbabwe ko kuma kar a taba yin sa ba, saboda abubuwa suna nan yadda suke. Masu rike da mukamai ne kawai zaben ya ke wa rana ba irinmu ba, a dangane da haka ban damu ba".

Sitz der Wahlkommision in Harare

Ofishin Hukumar zabe ta Zimbabwe

Idan har kotu ta amince da bukatar Mugabe ta dage zaben da makwanni biyu, za a gudanr da zaben ranar 14 ga watan Agusta ne maimakon ranar 31 ga watan Yuli da aka shirya gudanar da shi a yanzu. An dai gudanar da zabuka sau da dama a kasar ta Zimbabwe tun bayan samun 'yancin kanta tsahon shekaru 33, inda a koda yaushe sakamakon zaben na nuni da cewa jam'iyyar Shugaba Robert Mugabe ta Zanu PF ce ke lashe zaben. Mai shekaru 89 a duniya, Mugabe na daya daga cikin wadanda suka tsaya takara, inda zai fafata tsakaninsa da sauran 'yan takara ciki kuwa harda Firaminista a gwamnatin hadakar kasar kuma jagoran 'yan adawa Morgan Tsvangirai.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin