1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Motsin kasa ya haifar da tsoro a Abuja na Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB
September 7, 2018

A Najeriya Abuja fadar gwamnatin kasar ta fuskanci matsala ta motsin kasa da ke sanya gidaje motsi da ma rushewar wasu a unguwar Mpape abin da ya haifar da yanayi na tsoro.

https://p.dw.com/p/34Umu
Iran Erdbeben im Westen
Hoto: Maschreghnews

Wannan al'amati na motsin da kasa ke yi day a faru a unguwar ta Mpape amma kuma ake jinsa har a unguwani masu nisa da wurin irin su Maitama, Wuse two da ma Gwarimpa ya sanya tada hankali mazauna birnin na Abuja, musamman ma dai a Mpape inda a lokacin da abin ya faru ta kaiga mutane sun fita daga gidajensu yayinda wasu suka yi kaura suka bar unguwar kacokan.

Mpape dai dama unguwa ce da ke cike da duwatsu da kuma ramukan da manyan kamfanononin aikin hanya ke hakar kasa da ma fasa duwatsu. Tuni dai hukumar kai daukin gaggawa ta birnin Abuja ta fitar da sanarwa tana cewa abin da ya faru lallai motsi ne da kasa ta yi amma jama'a su kwantar da hankalinsu.

Da alamun dai mafi yawan mazauna yankin da ma wasu yankuna na Abuja da ke ci gaba da jin wannan motsi da kasa ke yin a cikin hali na dar-dar. Abinda ya sanya canke-canke a kan dalilin faruwar haka. Ba kasafai ake samun irin wannan yanayi a Najeriyar ba wacce.